1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga sun kashe mutane 46 a Kwango

June 12, 2023

Akalla mutane 46 sun halaka ciki har da yara yayin wani hari da 'yan bindiga suka kai wa wani sansanin 'yan gudun hijira dake Ituri a Arewa maso Gabashin Kwango.

https://p.dw.com/p/4SUQb
Hoto: Alexis Huguet/AFP/Getty Images

A cikin wata sanarwa rundunar sojojin wanzar da zaman lafiya ta MDD Monusco da ke Kwango ta yi tir da harin da ake dora alhakinsa a kan 'yan wata kungiya da ke gwagwarmaya da makamai a yankin na Arewa maso Gabashin Kwango.

Shaidun gani da ido sun ce maharan sun abka wa sansani 'yan gudun hijirar ne da ake kira Lala mai nisan tazarar kilomita biyar da sansanin Monusco a cikin dare Lahadi wayewar Litinin inda suka buda wuta.

Hare-hare 'yan bindiga masu nasaba da ta'addanci ko kuma fadan kabilanci ba bakon abu ba ne a Kwango, domin ko da a makon jiya wani harin ya yi ajalin mutane 12 a Arewa masu Gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango.