Kwango ta daukin hankalin jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 06.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Kwango ta daukin hankalin jaridun Jamus

Yarjejeniyar sulhunta rikicin Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango da shari'ar mataimakin shugaban kasar Equatorial Guinea Teodorin Obiang Nguema bisa zargin cin hanci a Faransa sun shiga kanun labaran wasu jaridun Jamus.

Cikin sharhin da ta yi mai taken fata na gari ga Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango, jaridar Süddeutsche Zeitung ta ce bakin alkali ya kama hanyar bushe wa shugaba Joseph kabila domin yarjejeniyar zaman ya haramta masa kwaskware kundin tsarin mulki ballata na ya samu damar zarcewa. Sai dai jariidar ta ce Inda gizo ke saka  shi ne rashin cimma matsaya kan furzunonin siyasa, lamarin da ke nuna cewar har yanzu da sauran rina a kaba.

A nata bangaren jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta mayar da hankali ne kan daya daga cikin 'yan siyasar Kwango da ya cancanci shugabantar kasar. Cikin sharhin da ta yi ta ce Kwango bata rasa 'yan siyasa da za su iya jagorantar kasar ba, daya daga cikinsu shi ne Moise Katumbi wanda ya ciyar da jihar Katanga da ke da arzikin karkashin kasa gaba a lokacin da rike mukamin gwamna.

Wani batu da ya dauki hankalin jaridun jamus shi ne na shari'ar mataimakin shugaban kasar Equatorial Guinea Teodorin Obiang Nguema da aka fara a Faransa bisa tuhumar almubazzaranci da kudaden jama'a. Cikin tsokaci da ta yi kan wannan batu, jaridar Berliner Zeitung ta ce bushashar da Teodorin Obiang Nguema ya yi ta yi ba wani abin mamaki ba ne, saboda mahaifinsa da ya shafe shekaru 37 yana shugabantar Equatorial Guinea ya mayar da baitilmali saniyar tatsa. Saboda haka ba za a rabu da bukar ba a fannin cin hanci d karbar rashawa a Equatorial Guinea ba domin arzikin man fetur da kasar take tinkaho da shi zai ci gaba da zama karkashin masu mulki da ‚yan korarsu.

Za mu karkare da sharhin da jaridar Die Tageszeitung ta yi kan harbe ministan muhalli da samar da ruwan sha na Burundi Emmanuel Niyonkuru har lahira da a ka yi a Bujumbura a jajiberen shiga sabuwar shekara. Ta ce miniistan na daga cikin manyan jami'an gwamnati da kungiyoyin farar ke zargi da mallakar dimbin filaye ba bisa ƙa'ida ba, lamarin da ya jawo masa bakin jini. Ta kara da cewa Niyonkuru ba shi ne kadai rikicin siyasa da Burubndi ke fama da shi ya yi ritsa da shi ba. Kashe-kashen ba gayra da dalili da kuma sace-sacen jama'ar da ma azabtarwa suna neman zama ruwan dare a Bujumbura. Wannan wata alama ce da ke nuna cewar ‘yan adawa da aka saba kashewa sun fara amfani da dabarun da aka san gwamnati da su wajen daukar fansa.