Kwango na so a janye dakarun kasa da kasa | Labarai | DW | 15.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kwango na so a janye dakarun kasa da kasa

Masharta dai na ganin har yanzu dakarun kasar ta Kwango ba su da kwarewar da zasu bada isasshiyar kariya ga fararen hula musamman a gabashin kasar da yaki ya daidaita.

Unterzeichnung Friedensabkommen im Kongo

Joseph Kabila: Shugaban Kwango

Shugaban Jamhuriyar Demokaradiyar Kwango ya bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta fara shirin janye dakarunta daga kasar bayan kwashe shekaru goma sha biyar na ayyukan wanzar da zaman lafiya. A lokacin da yake wani dogon jawabi a gaban 'yan majalisar dokoki a birnin Kinshasa, shugaba Joseph Kabila ya ce ya zuwa yanzu kasar ta samu kanta bayan tsawon lokaci na samun yakin basasa bi da bi.

Shugaba Kabila ya ce duk da cewa ana da 'yan tawaye a gabashin kasar ta Kwango wannan ba ya nufin za a ci gaba da ajiyar dakarun wanzar da zaman lafiya har 20 000 a kasar ta Kwango. Masu sharhi kan al'amuran yau da kullum na da ja kan ko dakarun kasar na da kwarewar da ta dace wajen ba da kariya ga fararen hula musamman a gabashin Kwango da yaki ya daidaita.