Kwango: Tshisekedi ya zama shugaban kasa
January 20, 2019Talla
Alkalin kotun tsarin mulkin kasar Luamba Benoit ya ayyana sakamakon:
"Da gagarumin rinjaye, jama'a sun zabi Mr Tshisekedi Tshilombo Felix a matasayin sabon shugaban Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango"
Sai dai gabatar da wannan sanarwa ke da wuya, abokin takararsa wanda kuma ke binsa da mafin yawan kuri'u Martin Fayulu, shi ma ya ayyana kansa a matsayin zababben shugaba na zahiri da jama'a suka zaba.
Magoya bayan Fayulu na zargin hadin baki tsakanin Felix Tshisekedi da Shugaba Joseph Kabila mai barin gado, na yin arangizon kuri'u, bayan gaza tabuka komai a bangaren dan takara na jam'iyyar mai mulki.