Kwango: Kabila ya lashe zaben ′yan majalisa | Labarai | DW | 12.01.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kwango: Kabila ya lashe zaben 'yan majalisa

A Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, kawancen masu mulki ya yi ikirarin samu kejeru 350 daga cikin 485 a zaben 'yan majalisar dokokin kasar da aka gudanar a jumulce da na shugaban kasa. 

Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ce kakakin gwamnatin kasar Lambert Mende ya sanar da shi a wannan Asabar cewa kawancen masu goyon bayan Shugaba Joseph Kabila ya yi wa kawancen Lamuka na jagoran adawa Martin Fayulu fintinkau  fintinkau a zaben 'yan majalisar dokokin inda ya ce dan takarar adawar ya samu kujeru 80 kawai a yayin da kawancen jam'iyyu na Cach wanda ya mara wa Felix Tsisekedi baya, ya tashi da kujeru kimanin 50. 

Wannan dai na nufin cewa bayan rantsar da shi Shugaba Tshisekedi wanda shi ne ya lashe zaben shugaban kasa zai zabi firaministansa daga cikin magoya bayan tsohon Shugaba Joseph Kabila wanda shi ne ke da rinjaye a majalisar. Sai dai dan takarar adawa Martin Fayulu ya yi watsi da sakamakon zaben tare ma da kalubalantarsa a gaban kotun tsarin mulkin kasar a wannan Asabar. 

Akwai dai sauran kujerun 'yan majalisa 15 da 'yan takarar za su fafata a watan Maris a yankunan da aka dage zaben na ranar 30 ga watan Disemba a bisa dalillai na tsaro. Ya zuwa yanzu dai hukumar zaben kasar ba ta ce uffan ba kan wadannan alkalumma da kakakin gwamnatin kasar ya wallafa.