An kwashe jami'an tsaro saboda barazanar tsaro
November 26, 2019Hukumar Lafiya ta Duniya wato WHO ta ce, ta kwashe ma'aikatanta da ke aikin bayar da riga-kafin cutar Ebola a yankin Beni na Jamhuriyyar Dimokradiyar Kwango bayan da aka fuskanci barazanar da rayuwarsu ke ciki na tsaro. An gaggauta amfani da wani karamin jirgin sama a aikin kwashe ma'aikatan su 49 daga garin zuwa birnin Goma ne daren jiya Litinin.
Hukumar dai ta yi gargadin halin da za a sami kai ciki, muddun matsalar tsaro ta ci gaba da haifar da tsaiko ga aikin dakile cutar mai saurin kisa, inda ta nemi a yi hattara.
Yankin na Beni na daya daga cikin yankunan Jamhuriyyar Kwango da ke fama da tsananin rashin tsaro amma kuma ke fama da annobar cutar Ebola. A baya-bayan nan, fararen hula kusan saba'in da bakwai aka kashe a wani hari da aka kai a farkon wannan watan na Nuwamba. An kiyasta cewa, cutar ta Ebola ta lakume rayukan mutum sama da dubu biyu.