Yunkurin kawo karshen matsalar tsaro a Kwango
September 22, 2022Talla
Fadar Elysée ta birnin Paris ta ce Shugaba Kagame na Ruwanda da takwaransa Félix Tshisekedi na kasar Kwango sun yi tattaunawar keke da keke karkashin jagorancin Shugaba Emmanuel Macron na Faransa, kana shugabannin biyu sun kama hanyar sulhunta rikicinsu da batun samar da zaman lafiyar da ya buwa a yankin gabashin Kwango, yankin da kungiyar M23 mai tada kayar baya ke cin karenta ba babbaka.
Bayan M23 kasashen biyu, sun kuma bayyana anniyarsu ta tunkarar barazanar tsaron da kungiyar ADF mai ikrarin jihadi a yankuna da dama na Jamhuriyar Dimkuradiyyar Kwango ke yi a yayin taronsu na su a birnin New York.