Kwango da M23 sun watse baram-baram | Labarai | DW | 12.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kwango da M23 sun watse baram-baram

Gwamnatin Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kwango da 'yan tawayen ƙasar wato M23 sun gaza cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakaninsu a zaman da suka yi a Yuganda.

Gwamnatin Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kwango da kuma Ƙungiyar tawaye ta M23 sun ɗage lokacin da za su rattaɓa hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya bayan da hukumomin Kinshasa suka buƙaci ƙarin lokacin domin yin nazari. Da farko dai jami'an dipolomasiya na ƙasashen Turai da kuma manyan jami'an gwamnatin Yuganda sun yi fatan ganin sassa biyu sun sa hannu a kan wannan yarjejniya shekara guda bayan fara zaman tattaunawa.

Kakakin gwamnatin Yuganda ya bayyana cewar an samu rashin fahimta daga ɓangaren gwamnatin Kwango game da suna ko taken da ya kamata a bai wa wannan yarjejeniya. Har yanzu dai ba a san lokacin da ɓangarorin biyu za su sake zama don rattaɓa hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiyar ba. Da ma ana ganin cewar ita ce za ta iya kawo ƙarshen rikicin da yankin gabashin Kwango ya shafe shekaru ya na fama da shi.Tun dai kwanakin da suka gabata ne dakarun gwamnati suka yi ta samun nasara a kan 'yan tawaye inda suka yi nasarar fatattakarsu daga gabashin ƙasar ta Kwango.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Abdourahamane Hassane