Kwango Brazaville ta yi sulhu da ′yan tawaye | Labarai | DW | 23.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kwango Brazaville ta yi sulhu da 'yan tawaye

Gwamnatin Kwango Brazaville ta cimma yarjejeniyar zaman lafiya da 'yan tawayen Pool da ke kudancin kasar watanni 20 bayan fara takaddama tsakaninsu.

Gwamnatin Kwango Brazaville ta sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta da 'yan tawayen yankin Pool wadanda suka fara tayar da kayar bayan zaben shugaban kasa na watan Afirilun 2016 . Dama rikici tsakanin sassa biyu ya hana gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki a mazabu da yawa kudancin kasar ta Kwango.

 'Yan tawayen da ake yi wa lakabi da 'ya'yan Pastor Ntumi sun yi alkawarin mika makamansu, yayin da gwamnati ta yi alkawarin shigar da su cikin rundunar sojojin kasar bayan sun kwance damarar yaki.

Mutane dubu 138 ne suka shiga cikin mawuyacin hali a wannan kasa ta tsakiyar Afirka, bayan da 'yan tawayen suka fara kai hare-hare. Sannan tashin hankalin ya sa zirga-zirgar jiragen kasa ta tsaya cik tsakanin manyan biranen kasar wato Brazaville da Pointe Noire (Puwent nuwar)