1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An raba mukamai tsakanin jam'iyyun hadaka a Kwango

Zulaiha Abubakar MNA
August 26, 2019

Watanni bakwai bayan rantsar da shugaba Felix Tshisekedi a matsayin shugaban kasa an sanar da sabuwar gwamnatin hadaka a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango.

https://p.dw.com/p/3OTQS
Demokratische Republik Kongo | Félix Tshisekedi | Provinzparlament Upper Katanga
Hoto: Presidence RDC/G. Kusema

Shugaba Tshisekedi ya rattaba hannu kan dokar gwamnatin hadaka tsakanin mambobi 23 daga jam'iyyarsa, da kuma mambobi 42 daga jam'iyyar tsohon shugaban kasar Joseph Kabila wanda ke da tarin magoya baya a kasar.

Yayin da yake yi wa manema labarai karin haske Firaminista Sylvestre Ilunga ya bayyana cewar bangaren gudanarwa zai rabauta da mukaman mataimakiyar firaiminista mace da kuma ministan harkokin kasashen ketare da tsare-tsare.


Shugaba Tshisekedi dai ya yi nasarar lashe zaben shugabancin kasar a karon farko da sauyin gwamnati ya gudana lafiya a  Kwango tun bayan samun 'yan ci daga kasar Beljiyam.