1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwango: An sanar da dage zaben wasu yankuna

Zulaiha Abubakar
December 26, 2018

Hukumar zabe a Jamhuriyar Demokradiyar Kwango ta sanar da dage ranar zabe a yankuna biyu na kasar zuwa watan Maris din sabuwar shekara sakamakon bullar cutar Ebola.

https://p.dw.com/p/3AeT7
DRC Präsident Joseph Kabila
Hoto: Reuters/K. Katombe

Yankunan da abin ya shafa sun hada da Beni da Butembo da Yumbi da kuma Mai-Ndombe da ke arewa da kudu maso yammacin kasar. Wannan sanarwa ta kara harzuka bangaren 'yan adawa wadanda tun a baya suka bayyana shakku game da amfani da na'urar zabe, batun da hukumar ta yi watsi da shi bayan ta ba al'ummar kasar tabbacin ranakun sanar da sakamakon zabe da kuma rantsar da sabon shugaban kasar a ranar 15 da 18 ga watan Janairun sabuwar shekara.

Ita dai kasar Kwango wacce ta kasance ta biyu a girma cikin kasashen Afirka ba ta taba mika mulki cikin kwanciyar hankali ba tun bayan samun 'yancin kai a shekara ta 1960.