1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ministan shari'ar kasar kwango na hannun 'yan sanda

Binta Aliyu Zurmi
June 27, 2020

Rahotanni daga Jamhuriyyar Dimukuradiyyar Kwango na nunar da cewa jami'an 'yan sandan kasar sun damke ministan shari'a Celestin Tunda a Kinshasa babban birnin kasar.

https://p.dw.com/p/3eRYe
Kongo Wahl Polizei Symbolbild ARCHIV
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Delay

Minista Tunda wanda ke rike da mukamin mataimakin Firaminista a gwamnati mai ci ta Shugaba Felix Tshisekedi ya mika kansa ne ga jami'an, bayan da aka kwashe tsawon lokaci suan yi wa gidansa kawanya.

Har ya zuwa wannan lokacin babu wani cikakken bayani dangane da laifin da ake tuhumarsa da aikatawa.