Kwango: An kama wanda ya kashe jami′an Majalisar Dinkin Duniya | Labarai | DW | 30.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kwango: An kama wanda ya kashe jami'an Majalisar Dinkin Duniya

Rahotanni daga Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango na cewa an kama mutumin da ake zargi da kitsa kisan wasu jami'an majalisar dinkin Duniya guda biyu a yankin Kasai na tsakiyar kasar a watan Maris da ya gabata. 

Kakakin rundunar sojin kasar ta Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango a yankin Kasai, Laftanal Anthony Mualushayi, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa an kama mutumin ne mai suna Constantin Tshidime Bulabula, a daren Juma'a washe garin ranar Asabar a mabuyarsa ta wani dakin karkashin kasa na wani kauye mai suna Bena Mpongo inda ya tare da wata mata.

Kotun kasar ta Kwango na mai zargin Tshidime Bulabula da bai wa kungiyar mayakan sa kai na yankin umurnin kisan jami'an Majalisar Dinkin Duniya Michael Sharp dan kasar Amirka da Zaida Catalan dan asalin kasashen Sweden da Chili, wadanda babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya ya wakilta a yankin na Kasai domin gudanar da bincike kan kisan da ake yi wa jama'a a yankin.