Zaman zullumi kan zaben Dimukuradiyyar Kwango
January 5, 2019Talla
Hukumar zaben kasar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ta jinkirta sakamakon zaben da ta niyyar sanarwa gobe Lahadi, inda ta kara mako guda kamar yadda shugaban hukumar Corneille Nangaa ya tabbatar. Nangaa ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa suna kokari amma tilas su kara mako guda.
Hakan ya zo ne daidai lokacin Cocin Katolika na kasar ke gargadin hukumar zaben ta fitar da sakamakon na zahiri maimakon sauya abin da mutane suka zaba.
Zaman zulumin da ake yi a kasar ta Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango yayin da ake jiran sakamakon zabe ya sanya Shugaba Donald Trump na Amirka turo sojojin 80 zuwa kasar Gabon domin kare ofishin jakancin Amirka a Kwango din inda aka samu wata hatsaniya.