Kwanaki 100 na sabuwar gwamnatin Mali | Siyasa | DW | 12.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kwanaki 100 na sabuwar gwamnatin Mali

A ranar huɗu ga watan Satumbar da ya gabata ne aka rantsar da sabon shugaban ƙasar Sai dai har yanzu ba a kai ga shawo kan rikicin da ƙasar ta Mali ke fama da shi ba.

Har kawo yanzu dai ba a kai ga magance tashe-tashen hankulan da ƙasar Mali ke fuskanta ba, duk kuwa da cewar a ƙarshen watan Nuwambar da ya gabata 'yan tawayen ƙungiyar MNLA na Abzinawa, sun ba da sanarawar cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakaninsu da gwamnati. Sai dai a zahirin gaskiyya abin ba haka yake ba, domin kuwa ana ci gaba da samun musayar wuta tsakaninsu da sojojin ƙasar, abin da masana ke bayyana wa da wani koma baya ga gwamnatin sabon shugaban Ibrahim Boubacar Keita., da a yanzu haka ya samu tsahon kwanaki 100 a kan karagar mulki.

Har yanzu da sauran aiki wajen biyan buƙatun al' ummar Mali

Ba wai matsalar rikici da 'yan tawayen Abzinawa da ƙasar Mali ke fama da shi ne kawai ke zama ƙalubale ga sabon shugaban ƙasar ta Mali Ibrahim Boubacar ba, har ma da wasu manyan matsaloli guda uku da suka haɗa da taɓarɓarewar tattalin arziki da ƙasar ke fama da shi. Tun bayan da ta tsunduma cikin rikici tsawon shekara ɗaya da rabi, sannan a kwai matsalar cin hanci da rashawa. A yanzu haka dai zaɓen 'yan majalisun dokoki zagaye na biyu da za a gudanar a ranar 15 ga wannan wata na Disamba da muke ciki, shi ne ka ɗai zai nuna irin yadda shugaban ƙasar zai ci gaba da samun goyon baya ko kuma matsin lamba daga 'yan adawa, tare da cewar a yayin zaɓen da aka gudanar a watan Satumbar da ya gabata, babu wata jam'iyya da ta samu nasarar kai tsaye. Shugabar kula da sashen Afirka a cibiyar bunƙasa ci gaban ƙasashe da ke birnin Bonn na nan Jamus, Julia Leininger, ta yi ƙarin haske dangane da abin da ya sanya gwamnatin Mali ta gaza magance matsalar cin hanci da karɓar rashawa.

T ce: "Batun yaƙi da cin hanci da karɓar rashawa shi ne abin da ƙasar Mali ta sanya a gaba, tun bayan da ta koma kan turbar demokraɗiyya a shekara ta 1992. Batun ne ma ya sanya aka zaɓi shugaban ƙasar a ƙarƙashin mulkin farar hula na farko, wato Amadou Toumani Touré, sai dai kuma ko da ya hau kan karagar mulkin ya gaza taɓuka wata rawar a zo a gani. Abin da ya sanya har yanzu aka gaza yaƙar cin hanci a kasar Mali shi ne, 'yan ƙasar na ganin a kwai cin hanci a tsakanin 'yan siyasar ƙasar wanda hakan ya sanya basu yadda da su ba".

Taɓarɓarewar al'amura tsaro na zaman cikasa ga ci-gaban ƙasar

A ɓangaren yaƙar masu aikata laifuka ma a ƙasar, ana yi wa batun kallon cewa akwai wasu 'yan siyasa da suke cin gajiyar aiyyukan da suke yi, ta hanyar sayar musu da makamai da muggan ƙwayoyi da kuma satar motoci, wanda hakan ya sanya aka gaza yakar su. Haka nan ma batun sasantawa da 'yan tawayen Abzinawa, duk kuwa da ƙokarin shawo kan matsalar da sabon shugaban ƙasar Ibrahim Boubacar ya ce yana yi. A cewar Georg Klute, masani kan al'amuran siyasa da na ƙasashen Afirka da ke jami'ar Bayreuth da ke nan Jamus, ya ce shi kansa Shugaba Boubacar ba shi da wani tunani mai zurfi wajen magance rikicin ƙasar ta Mali. Ya ce: "A zahirin gaskiyya ya zauna ne kawai ba tare da yin wani abun a zo a gani ba, domin shawo kan rikicin da ke tsakanin gwamnati da 'yan tawayen Abzinawa na MNLA da suke arewacin kasar. Bai yi wani hangen nesa ba wajen gano abin da ya haddasa rikicin domin shawo kansa cikin sauƙi".

Tun bayan da sojojin ƙasar Faransa suka kai ɗauki ga ƙasar ta Mali, sakamakon yunƙurin da 'yan tawaye masu kaifin kishin addini suka yi na ƙwace iko da ƙasar, tare da samun nasarar fatattakarsu, aka kasa samun zaman lafiya a yankin arewacin Malin, inda 'yan tawayen Abzinawa ke da ƙarfi, abin da kuma ya ke ci gaba da kawo tsaiko wajen dorewar zaman lafiya a baki ɗayan ƙaasar ta Mali.

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto haɗe da rahoton da Abdourahamane Hassane ya rubuta mana dangane da ziyarar da shugaban Mali ya kawo a nan Jamus

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Abdourahamane Hassane

Sauti da bidiyo akan labarin