Kwamitin sulhun MDD zai sake yin zama kan rikicin Somalia | Labarai | DW | 27.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kwamitin sulhun MDD zai sake yin zama kan rikicin Somalia

Kwamitin sulhun MDD ya kasa amincewa da wata sanarwa da ke yin kira da a tsagaita wuta sannan dukkan dakarun ketare su janye daga Somalia. Yanzu haka an shirya kwamitin sulhun mai membobin kasashe 15 zai sake yin wani zama a wani lokaci yau laraba inda zai shawarta akan rikicin na Somalia. Membobin kwamitin sun nuna adawa da wani daftarin sanarwa da kasar Qatar ta rarraba wadda ta yi kira ga dakarun kasashen waje musamman na Ethiopia da su janye. Dakarun Ethiopia na marawa gwamnatin wucin gadi mai hedkwata a garin Baidoa baya. Da farko wakilin MDD a Somalia Francois Lonsey Fall ya yi gargadi cewa rikicin Somalia na barazanar dagula harkokin tsaro a yankin kahon Afirka gaba daya.