Kwamitin da gwamnati ta kafa ya ce an yi karin gishiri ga alkalluman yawan mutanen da suka mutu a Baga. | Siyasa | DW | 01.05.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kwamitin da gwamnati ta kafa ya ce an yi karin gishiri ga alkalluman yawan mutanen da suka mutu a Baga.

Shugaba Jonathan ya karbi sakamakon binciken farko da sojoji suka gudanar domin gano mussabbabin tashin hankali Baga a jihar Borno da kuma zahirin asara da ya haddasa.

A wani abun dake zaman kokarin rage kaifin radadin adawar da ta mamaye harin da sojojin Tarayyar Najeriya su ka kai a garin Baga dake jihar Borno a cikin makon jiya, gwamnatin kasar ta karbi rahoton farko na wani kwamitin jami'an tsaron kasar da ta kafa, domin nazarin ainihin abun da ya faru a Baga.

Karkashin jagorancin babban hafsan tsaron kasar ta Nijeriya Admiral Ola Sa'ad Ibrahim,baki ya zo daya a tsakanin daukacin jami'an tsaron kasar da suka shaidawa shugaban cewa 'yayan Kungiyar ta Boko Haram 30 da kuma wasu gawawwaki Shida na farar hula ne kawai suka hallaka sakamakon harin dake zaman mafi kamari a bangaren sojan tun bayan tashin hankalin da ke cikin shekarar sa ta Uku.

Dr Reuben Abati dai na zaman kakakin gwamantin kasar mutumin kuma da ya sanar da sakamakon farko na binciken kwamitin na gwamnatin kasar.

A yayin da aka yi zargin cewar mutane 185 ne aka kashe a garin Baga , kwamitin ya samu bayanan babban Kwamandan rundunar hadin gwiwar kasa da kasa dake garin a ranar 24 ga watan Afirilu na shekara ta 2013 a inda ya shaida musu cewar an kashe 'yan ta'adda 30 a yayin batakashin sannan kuma an ga wasu gawwawaki shida a gefen Tafkin Chad dake kilomita uku daga garin.

Bayyanan 'yan kwamitin sun tambayi wasu 'yan garin ko za su kai su inda aka bunne gawawwakin mutane 185 mutanen suka ce ba su da masaniyar labarin kaburburan.

Shima shugaban karamar hukumar Kukawa an tambaye shi kan batun yace bashi da masaniya , kuma dama tun da farko shugaban karamar hukumar ya shaidawa yan kwamitin cewar musulmi ba su bunne fiye da gawa guda cikin Kabari.

Don gane da batu na kaddarori da gidaje dai ga abunda kakakin cewar ya gani cikin rahoton da ya ce na zaman na farko cikin jerin rahotanni da gwamntin kasar ta tsara karba kan harin.

"Kafafen yada labarai sun kuma ce an kona gidaje sama da dubu uku, amma kuma daga nazarin 'ya'yan kwamitin duk da cewar an kona gidaje, amma adadin nasu bai kai yawan da ake batu ba, kuma yana da muhimmanci ku sani cewar gidajen da ake batu gidajen zana ne dake da saurin kama wuta. Kuma a fili take cewar, 'yan ta'addan na da alkadar kona wuri da zarar sun kai hari".

Sabon rahoton dai a cikin fatan gwmnatin kasar ta Najeriya zai rage kaifi na suka da adawar da take cigaba da fuskanta kuma ke barazana ga yunkurinta na tabbatar da hallascin matakin karfin tuwo ga 'yan fafutukar.

To sai dai kuma daga dukkan alamu akwai sauran tafiya musamman ma a idanun shugabanin siyasar jihar ta Borno da ke ganin harin da biyu da kuma ke bukatar tabbatar da hukunci kan daukacin masu ruwa da tsaki da kai harin a fadar Muhammad Tahir Monguno dake zaman dan Majalisar wakilai mai wakiltar garin na Baga.

ya zuwa yanzu dai an tsara ita ma Hukumar Kare Hakkin bil'Adaman ta Najeriya zata gudanar da nata binciken na musamman da nufin sanin ainihin abun da ya faru a Baga.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita:Yahouza Sadissou Madobi

Sauti da bidiyo akan labarin