Kwame Nkrumah: Jagoran ′yanci a Ghana | Tushen Afirka: mutanen da suka taka rawa a tarihin Afirka | DW | 13.06.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Tushen Afirka

Kwame Nkrumah: Jagoran 'yanci a Ghana

Kwame Nkrumah shi ne shugaban kasar Ghana na farko, bayan jagorantar kasar wajen samun 'yancin kai. Ya samu gogewa a matsayin malamin makaranta a kasashen Amirka da Ingila.

Rayuwa: 

An haife shi a ranar 21 ga watan Satumba 1909 a Nkroful da ke Ghana sannan ya rasu a ranar 27 ga watan Afrilun 1972 a birnin Bukarest na kasar Romeniya.

 

Abubuwan da suka sa ya shahara: 

Fafutuka wajen ganin lamura sun yi kyau a Afirka da taimakawa wajen nema wa Ghana 'yancin kai (a 1957), sannan ya kasance firaminista da shugaban kasa na farko a Ghana kafin a yi masa juyin mulki a shekarar 1966. Nkrumah ya ba da gudunmawa wajen kafa kungiyar kasashen Afirka ta OAU wadda aka sauya mata suna zuwa AU.

 

Abubuwa da suka jawo masa suka:

Tausayawa 'yan Socialist da kuma kiran kansa da ya rika yi a matsayin dan gurguzu. Wannan abubuwa sun jawo masa bakin jini a ciki da wajen kasar. Wasu ma na ganin Amirka ce ummul aba'isin matsalolin da ya fuskanta.

A dubi bidiyo 01:37

Kwame Nkrumah: Jagoran kwatar 'yancin kasar Ghana

Karfafa gwiwa da musayar ra'ayi:

Ya shiga an dama da shi a fafutukar da Amirkawa da ke da tushe daga Afirka suka rika yi sannan ya hadu da Martin Luther King a lokacin da yake Amirka. Baya ga wannan ya kuma hadu da fitaccen mai rajin kare hakkin dan Adam din nan kana masanin ilimin halayyar dan Adam wato W.E.B. Dubois. A lokacin da yake yin karatu a Birtaniya, Nkrumah ya hadu da 'yan uwansa 'yan Afirka da ke fafutukar nema wa kasashensu mulkin kai. Wadannan mutane sun hada da Jomo Kenyatta na Kenya da Haile Selassie na Habasha da kuma Hastings Banda na Zambiya.

 

Fitattun Kalamansa:

"Ba za mu dubi gabas ko yamma ba: Za mu dubi gabanmu ne."

"Mutane da suka san abin da suke yi kuma za su iya jajircewa ne kan shirya juyin-juya hali."

"'Yanci ba wani abu ne da za a iya cewa wani zai ba da shi kyauta ga wani ba. Mutane kan rike shi a matsayin nasu kuma ba wanda zai iya karbe shi daga hannunsu.''

 

Cece-kuce:

A shekarar 2012 aka sanya mutum-mutumin Nkrumah a shalkwatar kungiyar kasashen Afirka ta AU da ke birnin Addis Ababa na kasar Habasha. Mutane da dama na aza ayar tambaya ta hikimar yin hakan. A kasar Habasha alal misali 'yan kasar na cewar zai fi dacewa a karrama tsohon shugaban kasar Haile Selassie kana a dauke shi a matsayin wanda ya aza ginshiki na girka kungiyar AU. Firaministan Habasha na wancan lokacin Meles Zenawi ya yi wani jawabi kan wannan batu, inda ya kare dalilai na sanya mutum-mutumin Kwame Nkrumah maimakon na Haile Selassie.

 

Karkashin shirin na musamman da DW kan tsara na Tushen Afirka bisa tallafi na gidauniyar Gerda Henkel.

Sauti da bidiyo akan labarin