1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwale-kwale ya nitse da mutam 100 a Kwango

Abdul-raheem Hassan MAB
October 9, 2021

Ana zaton fiye da mutane 100 sun mutu ko sun bace bayan nitsewar kwale-kwale guda tara da ke hade da juna, yayin da mutane 39 suka tsira.

https://p.dw.com/p/41TUv
Demokratische Republik Kongo | Boot auf dem Kongo nahe Mbandaka
Hoto: Junior Kannah/AFP/Getty Images

Hukumomin agaji sun gano gawarwaki 61 daga ranar Llitinin zuwa Talata, sannan ana ci gaba da neman wasu mutane  60 da suka bace, kamar yadda Nestor Magbado, kakakin gwamnan lardin Mongala da ke Arewa maso yammacin kasar ta Kwango ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP.

Hukumomi sun ce hadarin kwale-kwalen na da nasaba da cunkoson kaya da jama'a da kuma rashin kyawun yanayi. Wannan shi ne karo na baya -bayan nan a jerin hadurran ruwa a Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango, inda mutane kan yi tafiye -tafiye a cikin jiragen ruwa masu yawa da marasa lafiya.