Kwalambiya: Za a fara binciken ′yan FARC | Labarai | DW | 15.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kwalambiya: Za a fara binciken 'yan FARC

Hukumomin shari'a za su fara bincike domin fara shari'a kan laifukan yaki da ake zargin 'yan tawayen FARC da aikatawa a yakin basasar da aka kwashe sama da shekaru 50 ana yi.

A wani mataki na cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin gwamnatin Kwalambiya da 'yan tawayen FARC, gwamnati ta fidda shirin da zai ba wa wadanda yakin ya shafa damar gabatar da kara. Sai dai ba'a tsaida lokacin fara sauraron ba'asin kararrakin da za a gabatar a gaban kotu ba.

Tun bayan da gwamnatin Kwalambiya ta cimma yarjejeniyar zaman lafiya da 'yan tawayen FARC a shekarar 2016, sama da tsoffin 'yan tawayen dubu 4,700 sun amince da ba wa kotun hadin kai wajen amsa laifukan su domin jajantawa wadanda abin ya shafa. Akalla mutane dubu 250,000 aka kiyasta suka mutu a yakin basarar kasar yayin da wasu dubu 60 suka bace babu labari.