Kwalamabiya: Paparoma na son a hada kai | Labarai | DW | 07.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kwalamabiya: Paparoma na son a hada kai

Shugaban mabyia darikar Katolika ta duniya Paparoma Francis ya ce zai yi amfanin da zariyarsa a Kwalambiya domin aikewa al'ummar kasar sakon da ya ke tafe da shi na neman hadin kai tsakanin al'ummar kasar.

Baya ga wannan batu, Paparoman zai kuma yi amfani da ziyarar ta sa wajen tattaunawa da Shugaba Juan Manuel Santos gami da bishof-bishof da ke jagorantar 'yan darikar Katolika a kasar da kuma takwarorinsu na kasar Venezuwela wadda yanzu haka ke fama da matsi na tattalin arziki. Wannan ziyara da Paparoman ya fara dai ita ce irinta ta 20 da yi a kasashen duniya tun bayan da ya hau wannan matsayi a shekarr 2013 kuma wannan shi ne karo na 5 da ya ziyarci yankin Latin Amirka wanda ke zaman wajen da ya fito.