1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jami'an tsaro sun tarwatsa masu zanga-zanga a Kuwait

Zulaiha Abubakar
May 4, 2020

Ma'aikatar harkokin cikin gida a Kuwait ta bayyana cewar jami'an tsaro sun yi nasarar tarwatsa masu zanga-zanga 'yan kasar Masar, wadanda suka bukaci mahukunta daga Masar din su kwashe su daga kasar Kuwait.

https://p.dw.com/p/3bl6x
Fahne von Kuwait
Hoto: picture-alliance/Xinhua/Y. Lei

Ma'aikatar da kara da cewar kafin wannan lokaci masu zanga-zangar na tsare ne a wani matsuguni da kasar Kuwait ta yi tanadi domin killace wadanda ke zaune a kasar ba bisa ka'ida ba.

Alkaluman da hukumar yaki da cutuka masu saurin yaduwa a kasar ta Kuwait sun tabbatar da kamuwar akalla mutane 4,983 da cutar Covid-19 a fadin kasar yayin da wasu 38 suka rigamu gidan gaskiya, batun da gwamnatin kasar ta bayyana a matsayin hujjar daukar tsauraran matakai a kan wanda aka samu da karya dokar zaman gida.

A nasu bangaren jami'an huldar jakadancin Masar a Kuwait sun gana da masu boren, tare da daukar musu alwashin kawo jirgin da zai fara jigilar mata da yara kanana batun da wasu daga cikin masu zanga-zangar suka bayyana shakku.