Kuri′ar raba gardama ta zo da bazata a Kwalambiya | Labarai | DW | 03.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kuri'ar raba gardama ta zo da bazata a Kwalambiya

Dukkanin wadanda suka jagoranci shirin zaman lafiyar wato Shugaba Juan Manuel Santos na Kwalambiya da jagoran 'yan tawayen na FARC Timochenko sun sha mamakin sakamakon.

Al'ummar kasar Kwalambiya sun yi fatali da yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin gwamnatin kasar da 'yan tawayen juyin juya hali na Kungiyar FARC, abin da ke zuwa bayan samun rinjaye ba mai yawa ba tsakanin masu cewa sun aminta da 'yan bama yi a kuri'ar raba gardama da aka kada a ranar Lahadi.

Bayan tattara sakamako na kashi casa'in da tara cikin dari na kuri'un raba gardama da aka kada, sakamakon ya nunar da cewa kashi 50.2 sun nuna kin amincewarsu da 'yan tawayen na FARC masu ra'ayin Makisanci su shigo cikin al'umma su saje, yayin da kashi 49.7 suka amince.

Rikicin da 'yan tawayen a gwamman shekaru ya kai mutane 220,000 lahira yayin da miliyan takwas suka kaurace wa muhallansu.