Kura-kuran zabe a Najeriya da yadda za a yi gyara kansu
April 9, 2015Talla
A zaben ranar 28 ga wata Maris da ya fidda janar Muhammadu Buhari a matsayin zababben shugaban kasa da 'yan majalisun kasa, an sami matsaloli daban-daban da suka sanya kiraye-kiraye ga hukumar zaben kasar ta yi hanzarin yin gyara don kyautata aikin baki dayansa.
Wani ma abin dake daukar hankali shi ne na yadda jam'iyyarPDP ke dishewa a siyasance, bayan shan kayeda shugaba Jonathan ya yi a zaben, lamarin da ya sanya da dama daga cikinjigogi da magoya bayan jam'iyyarke ficewa suna shiga APC.
Mun tsara jerin rahotannin da suka dubi wadannan batutuwan da muka bayyana.