Kungiyar IS na barazanar hallaka wasu | Labarai | DW | 27.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar IS na barazanar hallaka wasu

Kungiyar IS ta ce cikin sa'o'i 24 masu zuwa, zata halaka wani dan kasar Japan da ma wani matukin jirgin sama dan kasar Jordan da suke garkuwa dasu.

Cikin wata sanarwar da kungiyar ta fitar ta kafar sadarwar Intanet a yau Talata, kungiyar ta sake kiran da a sako 'yar kasar irakin nan Sajida Al-Rishawa da aka yankewa hukuncin kisa a kasar Jordan saboda samunta da laifin kasancewa cikin wani harin ta'addanci da ya kashe mutane 60 cikin shekara ta dubu biyu da biyar.

Sakon da ya fito ta faifan bidiyo, ya yi kama da wata dakungiyarta sako a karshen makon jiya, sai dai babu daya daga cikin sakonnin dake dauke da alamar kungiyar.Sai dai an nuno foton da ba na bidiyon ba da ya nuno gangan jikin Haruna Yukawa, wato dan kasar Jordan. Kamfanin dillacin labaran Associated Press da ya ruwaito labarin ma, ya ce bai tantance sabon faifan bidiyon ba.