'Yan cirani: Kungiyar EU na neman mafita
June 20, 2018Talla
Matakin tattaunawar ya biyo bayan kiran da shugaban EU Jean-Claude Juncker ya yi sakamakon yadda batun 'yan ciranin ke yunkurin haddasa rarrrabuwar kai a tsakanin kasashen da ke cikin kungiyar. Cece-kucen da ya kutso kai a baya-bayan nan shi ne yadda gwamnatin hadakar Jamus ta Angela Merkel ke fuskantar matsin lamba sakamakon ba 'yan gudun hijira sama da miliyan daya mafaka tun a shekara ta 2015, lamarin da har yanzu ya ke cigaba da janyo mata bakin jini daga wasu bangarorin.