Kungiyar EU ta samu mamba ta 28 | Labarai | DW | 01.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar EU ta samu mamba ta 28

Shekaru 20 bayan da ta samu 'yancin cin gashin kanta daga kasar Yogosilabiya, kasar Croatia ta zamo daya daga cikin mambobin kungiyar EU.

Kasar Croatia ta samu nasarar zama mamba a kungiyar Tarayyar Turai wato EU, wanda hakan ya nuna cewa yanzu kungiyar na da mambobi 28 maimakon 27 da take da su a baya.

Dubban 'yan Croatia sun yi dandazo a babban birnin kasar Zagreb a daren jiya domin nuna farin cikinsu da kasancewar kasar tasu mamba a kungiyar ta EU.

Rahotanni sun bayyana cewa akallah kimanin manyan baki 100 daga sassa daban daban na nahiyar Turai ne suka samu halartar wani gagarumin biki da shugaban kasar ta Croatia Ivo Josipovic, ya jagoranta a fadar gwamnatin kasar.

Wannan nasarar ta zo ne shekaru 20 da samun 'yancin kai da Croatia ta yi daga kasar Yogosilabiya, bayan yakin da suka gwabza wanda ya yi sanadiyar asarar rayuka da dukiyoyi masu yawa.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Zainab Muhammad Abubakar