Kungiyar EU ta goyi bayan matakan Faransa a Mali | Siyasa | DW | 15.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kungiyar EU ta goyi bayan matakan Faransa a Mali

Hukumar Kungiyar Hadin Kan Turai tayi marhabin da matakan Faransa na hana yan tawaye su mamaye kasar Mali baki daya

Kungiyar TarayyarTurai ta yaba da matakin Faransa na kai dauki domin kare kasar Mali daga fadawa hanun masu kaifin kishin lslama, wannan yayin da Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya da gagarumin ringaye ya amince da matakin na kasar ta Faransa na kaddamar da farmaki kan mayakan Arewacin Mali, domin sake hade kasar.

Kungiyar ta kasashen Tarayyar Turai, wadda tunda fari ke shirin tura dakaru 200, domin horas da sojojin Mali, domin sake kwato yankin arewacin kasar, yanzu ta goyi bayan matakin Faransa na kaddamar da farmaki ta sama, domin dakile karfin 'yan tawayen wadanda ke rike da yankin arewacin kasar ta Mali. Pia Ahrenkilde mai magana da yawun kungiyar ta bayyana cewa:

"Wannan hali yana bukatar kasashen dunyia su kara himma, su kuma nuna cewa su na iya kara bada goyon baya ga Mali, domin sake tabbatar da ikon ta a daukacin kasar, da kuma sake dawo da doka da oda."

Mali Militäreinsatz 15. Januar 2013

Sojojin Mali cikin shirin yaki

Kuma wannan ya yi daidai da kalaman shugaban hukumar gudanarwa ta Kungiyar Tarayyar Turai, Herman Van Rompuy, wanda bayan ganawa da shugaban Masar Mohammed Mursi, yayin ziraya a birnin Alkahira, yace tilas, a dauki matakan dakile aiyukan ta'addanci:

"Nayi bayani kan matakin kasashen dunyia na kawar da aiyukan ta'adanci, da samun nasara kan 'yan tawaye da 'yan ta'adda, wadanda ke janyo wahala ga mutane. Yana da mahimmaci hukumomin Mali su samu galaba na iko da daukacin yankunan kasar da gudanar da aiyukan sasanta al'umma."

Yanzu za'a iya cewa, matakin na Faransa ya samu karbuwa daga sassan da su ka dace a samu hakan, kuma kwamishiniyar harkokin wajen kungiyar ta Tarayyar Turai Catherine Ashton, ta hanun kakakinta Michael Mann, ga abun da ta ke cewa:

"Wannan aiki ya kasance mai mahimmanci. Babu wani sauyi sai an samu nasara kan abun da aka saka a gaba."

Tuni ministan tsaron Jamus, Thomas de Maiziere, ya ce a shirye kasar ta ke wajen bada gudamawar kawar da 'yan tawaye da su ka mamaye yankin arewacin kasar ta Mali, wadanda yanzu kuma Faransa ke musu barin wuta ta sama:

"Jamus za ta baiwa sojojin da za su gudanar da aiki ilimi da horon da ake bukata, kamar yadda aka tsara karkashin Kungiyar Tarayyar Turai."

Van Rompuy PK beim EU Gipfel in Brüssel

Shugaban hukumar Kungiyar Hadin Kan Turai Van Rompuy

Kuma wannan ya yi daidai da ya goyon baya daga Majalisar Dinkin Duniya, inda bayan tattaunawa ta sa'o'i biyu jakadan Faransa a majalisar, Gerard Araud ya ce daukacin mambobin kwamitin na sulhu sun amince da matakin kai samame kan mayaka masu kaifin kishin Islama. Sannan ya kara da cewa an amince da gaggauta tura dakarun kasashen Afirka 3,000 cikin makonni masu zuwa, domin bada gudummuwar sake kwato yankin na arewacin Mali.

Tuni Sakatare Janar na Majalisar ta Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya yi lale marhabin da matakin da Faransa ta dauka na kare kasar ta Mali daga fadawa hanun mayakan masu kaifin kishin Islama. Rahotanni sun tabbatar da cewa harin na dakarun Faransa ta sama ya tilasawa mayakan ficewa daga birane masu yawa, kuma an hallaka da dama daga cikinsu.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu

Sauti da bidiyo akan labarin