Kungiyar Boko haram ta samu sabon suna | Labarai | DW | 23.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar Boko haram ta samu sabon suna

kungiyar daular Musulunci da ke Yammacin Afrika, shi ne sunan da kungiyar Boko haram ke kiranta kan da shi yanzu bayan da ta yi mubaya' a ga kungiyar IS.

Kungiyar da aka fi sani da suna Boko Haram ta sanya wa kanta wani sabon suna a lokacin da ta fitar wasu sabbin hotona na mayakanta. A wannan karon dai fuskokinsu a bude ya ke a wurare daban- daban sabanin yadda suke fitowa a baya fuskokinsu a rufe, sannan kuma karkashin sunan kungiyar Daular Musulunci da ke Yammacin Afrika wato "Islamic State in West Africa" a turance.

Boko Haram ta dai wallafa wadannan hotuna ne a shafin sada zumunci na internet kuma shi ne na farko tun bayan da a watan Maris, shugaban kungiyar ta Boko Haram Abubakar Shekau, ya bayyana mubaya'arsa ga kungiyar IS wacce ta yi ikirarin kafa daular Musulunci a yankunan Iraq da Syria.

Sai dai kuma a daya hannun dakarun Najeriya sun kutsa dajin nan na Sambisa da ake zaton nan ne cibiyar mayakan na Boko Haram, a wani abin da sojin ke cewa fafatawa ta karshe da suke sa ran yi da 'yan bindigar. Rundunar ta sojojin Najeriya ta yi ikirarin hallaka wani babban kwamandan Kungiyar Boko Haram a dajin Sambisa.