Kungiyar ASUU ta dakatar da yajin aiki | Siyasa | DW | 17.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kungiyar ASUU ta dakatar da yajin aiki

Yanzu dai da alamu baki yazo daya tsakanin kungiyar malaman jami'oin Najeriya ta ASUU da gwamnatin kasar abin da ya kai ga dakatar da yajin aikin da aka dade ana yi.

Bayan sama da watanni 5 dalibai na zaune a gidajen su sakamakon yajin aiki da kungiyar malaman jamia ta yi a Najeriya, yanzu haka dai kungiyar da ake wa lakabi da ASUU ta ayyana dakatar da wannan yajin aiki, lamarin dake nufin cewar yanzu dalibai zasu iya koma azuzuwa a cigaba da daukar darasu,sai dai kuma dalibai da masu fashin baki na ganin cewar yajin aikin bai amfana komai ba, illa dai kawai batawa dalibai lokaci da akayi.

A kwanakin baya ne aka cimma yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin gwamnatin Tarayyar Najeriya da kuma kungiyar ASUU ta malaman jami'a zalla, wanda hakan yasa kungiyar ta kira wani babban taro a birnin Minna na jihar Naija inda a nan ne ta ayyana dakatar da wannan yajin aiki, wanda ta shafe sama da watanni 5 tana yinsa. Sai dai kuma mutane da dama na ganin cewar wannan dakatar da yajin aiki na kungiyar an gudu ne ba a tsira ba, domin babu wata tartibiyar magana ta ceto ilimi daga halin ha ula'i da yake ciki a Najeriya, lamarin da wasu ke kallon yajin aiki a matsayin an gudu ba a tsira ba, domin Bahaushe kance gudun da babu tsira cikinsa kwanciya tafishi. Malam Yusufu Magaji masani ne akan ilimi, kuma mai fashin baki akan al'muran yau da kullum. Yace hakika an batawa daliban lokaci. To suma dai daliban na ganin cewar yajin aikin garesu dai bai amfana komai ba domin ya haddasa musu nannage a guri guda, kamar yadda wata daliba a jamiar Bayero ta Kano Fauziyya Abdulsalam ta bayyana.

Shima wani dalibi Kazeem Abdulhakim gareshi samma kal,domin yace badan yajin aikin bad a tuni yayi salllama da jam'ia.

Protestierende Studenten während ASUU Streik in Kano

Sulhu bayan zanga-zangar wakilan kungiyar ASUU

Sai dai kuma duk da cewar dalibai da iyaye na murnar komawa ga alama ba za ayi saurin yin murnar ba la a kari da kalaman wani malami a jami'ar Bayero ta Kano Dr Hamisu Miko dake cewar ai ba janye yajin aikin akayi ba dakatar dashi akayi dan haka da zarar an busa musu begilan zasu iya cigaba da yajin aikin.To koma dai menene,Yanzu haka har an fara shirye shiryen fara daukar darasu a jami'ar Bayero ta Kano anda hakan ke nufin cewar nan gaba kadan dalibai zasu fara shiga azuzuwa domin daukar darasu.