1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siri Lanka: Yankan kauna ga Firaminista

Lateefa Mustapha Ja'afar
November 14, 2018

Majalisar dokokin kasar Siri Lanka ta amince da kudirin yankan kauna a kan sabon Firaministan Sri Lanka Mahinda Rajapaksa da majalisar zartaswarsa.

https://p.dw.com/p/38Cqx
Mahinda Rajapaksa
Firaministan Siri Lanka Mahinda RajapaksaHoto: picture-alliance/Pacific Press/P. Dambarage

Rahotanni sun nunar da cewa matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da cece-kuce kan gwamnatin ta Rajapaksa a kasar. Kakakin majalisar wakilan kasar Karu Jayasuriya ya sake hada kan majalisar bayan da kotu ta bukaci da a sake gudanar da zabe a cikin watan Janairun shekara ta 2019 da ke tafe. Sai dai zaman nasu ya samu tsaiko daga jami'an gwamnati da ke yin zanga-zanga, abin da ya hana kakakin majalisar kirga kuri'un masu goyon bayan kudirin, sai dai ta hanyar lura da wadanda suka fi nuna goyon baya.