Kudin bai daya a Afirka ta yamma
October 25, 2013Shugabannin kasashe 15 na yammacin Afirka dake cikin kungiyar bunkasa tattalin arzikin Afirka ta yamma wato ECOWAS, na gudanar da wani taro na musamman a Dakar babban birnin kasar Senigal, domin duba batun yin kasuwancin bai daya da kuma samar da kudaden bai daya a tsakanin kasashen nan da shekara ta 2020.
Taron wanda ake sa ran zaifi mayar da hankali kan batun tattalin arzki, zai kuma duba batun rikicin kasashen Mali da Guinea-Bissau da kuma fargabar da ake yi ta barkewar rikicin bayan zabe a kasar Guinea Konakri.
Da yake zantawa da manema labarai gabanin taron a birnin Dakar na kasar Senigal, shugaban kungiyar ta ECOWAS Kadre Desire Ouedraogo, ya ce suna so su mai da hankali kan batun tattalin arziki a wanna karon, ba kamar a lokutan baya ba da kungiyar ta saba zamowa kan gaba wajen sasanta rikici da kuma al'amuran siyasa.
Mawallafiya:Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita:Usman Shehu Usman