Kuba: Zaben gyaran sabuwar majalisar wakilai
March 11, 2018A wannan Lahadin ce al'ummar Kuba ke gudanar da zabe don gyaran sabuwar majalisar wakilan kasar, a wani gagarumin yunkuri na daga matsayin sabon shugaban kasa, matakin da ke zama na farkon irinsa a tarihin Cubar cikin shekaru 60, a wajen iyalin Castro.
Sabbin 'yan majalisar dokokin ne ake saran za su zabi mutumin da zai gaji shugaba Raul Castro mai shekaru 86 da haihuwa, idan ya yi murabus a wata mai kamawa.
Castro ya kada kuri'arsa a gunduwar Santiago de Kuba da ke yankin kudu maso gabashin kasar, a yayin da mataimakinsa kuma wanda ake ganin zai gajeshi Miguel Diaz-Cane, ya yi nashi zaben a gunduwar Santa Clara da ke tsakiya.
A shekara ta 2006 nedai Raul Castro ya karbi ragamar mulkin kasar daga dan uwansa mara lafiya Fidel Castro, wanda ya mulki Kuban tun bayan kifar da gwamnati a shekara ta 1959.
Kimanin Cubawa miliyan takwas ne ke kada kuri'ar gyara majalisar wakilai 605, domin tabbatar da daidaito a wakilcin kasar.