Kowa nada ′yancin mallakar makami a Amirka | Labarai | DW | 16.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kowa nada 'yancin mallakar makami a Amirka

Maganar mallakar makamai a kasar Amirka na ci-gaba da jinyo rarabuwar kawuna a tsakanin al'ummar kasar,yayinda kuma jama'a ke ci gaba da sayen makaman.

Tun bayan da kashe kashe ke dada karuwa a kasar Amirka,jihar New York ce ke sahun gaba gurin daukar kwararan matakai domin shawo kan lamarin. Kodayake a dai hannu daya,jama'an kasar na ci-gaba da kokarin mallakar makaman inda rahotani suka bayana cewar tun bayan harbi a kan mai uwa da wabi da wani matashi ya yi a watan Disamban da ya shude a jihar Colorado,inda ya hallaka a kalla mutane 26 ciki har da yara 20,sama da bindigogi milyon daya ne aka sayar a kasar ta Amurka.
Ko a jiya Talata a jihar Kentucky,wani da ya ji dadin bindigar ya aika wasu mutane biyu har lahira. To saidai batun mallakar makaman na ci-gaba da haifar da kace ni ce a kasar abun da ya tilastawa shugaba Obama bukatar gabatar da wani kuduri na binciken masaya makaman a zauren wakillai da ma majalisar dattawa.
Masu adawa da mallakar makaman na ganin kudurin ba zai aiyana wani canji ba a lamarin matukara ba a kwaskwarimance ayar dokar nan mai lamba 2 ta kudin tsarin milkin kasar ba ,da ta baiwa kowane ba'amurke damar mallakar iya makaman da yake bukata,gyaran fuskan da ake gani kuma yana da matukar wahala wai gurguwa da auren nesa.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita : Mahammad Nasiru Awal