1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu Turai ta yi hukunci kan kaddama a Poland

Suleiman Babayo
October 19, 2018

Kotun Tarayyar Turai ta nemi Poland ta janye dokar rage shekarun ritaya ga alkalai da ya janyo cece-kuce kan sauye-sauyen da gwamnatin ta aiwatar tun shekara ta 2015.

https://p.dw.com/p/36rNV
Polen 2015 Verfassungsgerichtshof in Warschau
Hoto: picture-alliance/dpa/P. Supernak

Kotun Tarayyar Turai ta bukaci kasar Poland ta janye dokar rage yawan shekarun da alkalai za su yi ritaya a aiki daga kotun kolin kasar, domin kawo karshen sauye-sauyen da ta aiwatar masu cike da rudani.

Tun shekara ta 2015 aka shiga takun saka tsakanin Poland da Tarayyar Turai bisa wasu sauye-sauye abin da ya janyo zuwa kotun domin warware sabanin. Tun farko Poland ta rage yawan shekaru da manyan alkalai za su yi ritaya daga 70 zuwa 65 lamarin da ya haifar da cece-kuce bisa neman ganin wasu alkalai 22 sun ajyie aiki.