SiyasaAsiya
Kotun Thailand ta haramta babbar jam'yyar adawa
August 7, 2024Talla
Babbar kotun kasar Thailand ta yanke hukuncin rusa babbar jam'iyyar adawa ta kasar ta Move Forward Party, shekara guda bayan masu ra'ayin gaba-dai gaba-dai da suka kafa jam'iyyar sun samu nasarar lashe mafi yawan kujerun majalisar dokokin kasar fiye da kowace jam'iyya amma sun gaza samun nasarar iya kafa gwamnati, a kasar da ke yankin kudu maso gabashin Asiya.
Kotun tsarin mulki da ke birnin Bangkok fadar gwamnatin kasar ta yanke wannan hukunci na haramta jam'iyyar da Pita Limjaroenrat yake jagoranta, wanda shi kansa dan siyasar mai farin jini an yanke masa hukuncin hana shiga harkokin siyasa na shekaru 10.
Ita dai jam'iyyar adawar da aka haramta da musanta zargin da ake mata na raina masarautar kasar ta Thailand mai karfin fada aji.