Kotun Ruwanda ta karbi karar 'yan adawa da tazarce
September 9, 2015Kotun kolin Ruwanda ta bayyana halarcin karar da wata jam'iyyar adawar kasar ta shigar a gabanta ta na mai kalubalantar yunkurin Shugaba Paul Kagame na yi wa kundin tsarin milkin kasarsa kwaskwarima domin sake tsayawa takarar neman shugabancin kasar a karo na ukku.
Tuni kotun wacce ta bayyana wannan matsayi nata ta kuma tsaida ranar 23 ga wannan wata na Satumba a matsayin ranar da za ta bude zaman shari'a kan wannan batu.
Tun a cikin watan Yulin da ya gabata ne dai majalissar dokokin kasar ta Ruwanda ta kada kuri'ar amincewa da bukatar shugaba Paul Kagame wacce za a gudanar da zaben raba gardama a kanta a nan gaba a kasar domin bashi damar yin tazarce a kan karagar milkin kasar a wani sabon wa'adin na shekaru bakwai.
A makon da ya gabata dai kasar Amirka ta bayyana adawarta da wannan shiri na shugaba Kagame