Kotun Najeriya ta bayar da belin Sowore | Labarai | DW | 11.01.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotun Najeriya ta bayar da belin Sowore

Wata kotu a Abuja helkwatar Najeriya ta ba da belin fitaccen dan gwagwarmayar nan wanda ya jagoranci zanga-zangar neman juyin juya hali Omoyele Sowore kan kudi Naira milyan 20 da kuma mutane biyu da za su tsaya masa. 

Tun a jajiberen shiga sabuwar shekarar nan ne dai aka kame Sowere da mutane hudu kan zargin taro ba bisa doka ba, da kitsa yunkurin tunzura jama’a, zargin da ya musanta. Comrade Bako Abdul shugaban kungiyar Campaign for Democracy  ya ce belin da aka ba Sowore ya nuna cewa Najeriya ta fara inganta tsarinta na dimukuradiyya.


Wakilin DW a Abuja Uwais Abubakar Idris ya ce kotun majistare ta sanya ka'idar cewa Mr. Sowere ba zai bar Abuja ba, kuma dole ne a ranakun Litinin da Jumma’a ya kai kansa kotu ko da ba za a yi zaman shari’a ba har zuwa lokacin da za a kamala shari'ar.