Kotun Madagaska ta tabbatar da zaben Rajoel
January 8, 2019Talla
Kotun tsarin mulkin kasar Madagaska ta tabbatar da sahihancin zaben Andry Rajoelina a zaben shugaban na watan Disemban da ya gabata, tare kuma da yin watsi da duk jerin korafe-korafen da abokin hamayyarsa Marc Ravalomanana ya shigar a gabanta domin kalubalantar sakamakon zaben.
Shugaban hukumar zaben kasar ta Madagaska.Jean-Eric Rakotoarisoa, ne ya tabbatar da hakan a wannan Talata a karshen zaman da kotun ta yi.
Hukumar zaben kasar dai ta ce dan takara Rajoelina ya samu kaso 55 da digo 66 daga cikin dari a yayin da abokin hamayyarsa Ravalomanana ya samu kaso 44 da digo 34 daga cikin dari na kuri'un da aka kada.