1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun ta hana Guaido fita daga Venezuela

Abdul-raheem Hassan
January 30, 2019

Matakin ya biyo bayan bukatar da babban mai gabatar da kara na bangaren gwamnati Tarek William Saab ya gabatar, kan rufe kadarorin shugaban adawar tare da haramtamasa fita wajen kasar.

https://p.dw.com/p/3CPeD
Venezuela Caracas Juan Guaido
Hoto: Getty Images/AFP/Y. Cortez

Umarnin kotun ya bukaci killace asusun madugun adawar kasar Juan Guaido da ke ikirarin zama shugaban rikon kwarya har sai an kammala bincike kan rikin siyasar kasar.

Magoya bayan gwamnatin Shugaba Nicolas Maduro sun ce matakin zai ba da damar kaddamar da binciken laifukan take doka da gudanar da haramtacciyar gwamnati karkashin shugaban 'yan adawar kasar Guidon.

Rikicin siyasar Venezuela na dada daukar zafi ne bayan da manyan kasashen duniya ke daukan bangare tsakanin Maduro da kuma Guido, inda Amirka da ke marawa jagoran adawar baya ta sa wa kamfanin man kasar takunkumi tare da fifita shugaban adawar kan ikon da kadarorin gwamnatin kasar da ke Amirka, amma kawayen Maduro kamar China da Rasha sun yi Allah wadai da mataki.