1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An hana shugaban Guatemala aiwatar da manufa

Suleiman Babayo
January 9, 2019

Babbar kotun kasar Guatemala ta toshe matakin Shugaban kasar na fatattakar hukumar yaki da cin hanci ta Majalisar Dinkin Duniya.

https://p.dw.com/p/3BHMP
Guatemala | Aurora Airport | Fall Yilen Osorio
Hoto: picture-alliance/dpa/AP Photo/M. Castillo

Babbar kotun kasar Guatemala ta toshe matakin Shugaba Jimmy Morales na yin gaban kai kan kawo karshen aikin hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai yaki da cin hanci da rasha a kasar.

Shugaban ya fusata bisa matakin hukumar na gudanar da bincike a kansa da 'ya'yansa maza gami da dan-uwansa, zargin da suka musanta. Kotun tsarin mulkin kasar ta Guatemala ta kwashe tsawon dare kafin samun matsayin. A shekaru 11 da hukumar ta yi ta gano zage-zarge cin hanci da rasha da suka shafi kimanin mutane 680 da suka hada da 'yan kasuwa, da zababbun wakilan al'uma gami da jami'an gwamnati.