Kotun Amirka ta amince da allurar mutuwa | Labarai | DW | 29.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotun Amirka ta amince da allurar mutuwa

Alkalan kotun kolin Amirka suka ce yin allurar sinadarin Midazolam wajan zartar da hukuncin kisa bai sabawa kundin tsarin mulkin kasarsu ba.

Kotun Kolin kasar Amirka ta tabbatar da halarcin matakin zartar da hukuncin kisa ta hanyar yi wa fursuna da aka yankewa hukuncin kisa allurar sinadari Midazolam da nufin sanyashi dogon barci kafin a yi mashi allurar mutuwa.

Alkalai biyar daga cikin tara suka amince da matakin wanda suka ce bai sabawa kundin tsarin milkin kasar ta Amirka ba, kuma sun kafa hujjarsu da cewa wadanda suka kalubalanci matakin a gaban kuliya ba su bada wasu hujjoji kwararara ba da ke nunar da cewa mutumin da aka yi wa allurar mutuwar na shan wahala kafin ransa ya fita ba.