Kotu za ta saurari shugabar Koriya ta Kudu | Labarai | DW | 04.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotu za ta saurari shugabar Koriya ta Kudu

Park Geun-Hye Shugabar Koriya ta Kudu, ta amince ta mika kanta ga ma'aikatar shari'ar kasar domin a saurare ta sakamakon badakalar cin hanci da ta taso a kasar.

Shugabar kasar dai ta karyata rade-radin da ake na cewa tana da wata alaka da Madame Choi, mai fada a ji a tsakanin magabatan kasar. Wannan badakala dai ta saka wani babban shamaki na kin yarda tsakanin al'ummar Koriya ta Kudun da Shugaba Park, wadda kasa da shekara daya kacal ya rage ta kawo karshen wa'adin mulkinta.

'Yan kasar da dama dai sun yi zanga-zangar nuna kin jinin shugabar kasar tare da neman ta yi murabus, abun da ya kai ga sauke Firaministan kasar. Wani binciken jin ra'ayin jama'a na Gallup da aka wallafa a wannan Juma'a, ya nunar cewa farin jinin shugabar kasar ya zube kasa warwas ya zuwa kashi biyar cikin 100.