Kotu ta yi watsi da shari′ar Julius Malema | Labarai | DW | 04.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotu ta yi watsi da shari'ar Julius Malema

Kotu a Afirka ta Kudu ta yi watsi da shari'ar da ake yi wa madugun 'yan adawar kasar Julius Malema wanda aka gurfanar kan zargin cin hanci da rashawa da kuma halasta dukiya haram.

Mai shari'a Billy Mothle ya ce kotu ta yanke shawarar watsi da karar bayan da masu gabatar da karar suka yi ta jan kafa da kuma kin amincewa da suka yi na a yi wa Mr. Malema din shari'a ba tare da guda daga cikin wanda ake zargi ba.

Shari'ar wadda aka somo ta shekaru 3 da suka gabata ta fuskanci tsaiko matuka bayan da guda daga cikin wanda ake zargi ya kwanta rashin lafiya, dalilin da ya sanya bangaren masu kara suka rika neman a dage shari'ar.

Jim kadan bayan kammala zaman kotu, Mr. Malema ya shaidawa manema labarai cewar dama can zargin da ake masa bai da tushe balle makama kuma a shirye ya ke nan gaba ya sake gurfana gaban kotu idan har sun sake yake shawarar gurfanar.