Kotu ta yankewa Silvio Berlusconi hukuncin ɗaurin shekara guda. | Labarai | DW | 07.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotu ta yankewa Silvio Berlusconi hukuncin ɗaurin shekara guda.

Tsohon firaministan na Italiya,na fuskantar matsin lamba na shari'a a daidai lokacin, da ake shirin gudanar da zagaye na biyu na zaɓuɓɓuka a ƙasar.

Kotu da ke a birnin Milan ta yanke masa hukuncin ne,bayan da ta sameshi da laifin a kan keta hadin bayyanan siri na bincke na alƙalai. A kan wata tabargarza ta cin hancin, a cikin wata harkar ta sayar da hannu jarin wani banki a shekarun 2005 wanda ya yi hira da wani ta waya talho.

Kotun dai, ba za ta iya kama tsohon firamistan ba, sai dukkanin hanyoyin da ya ke da sukunin samu na ɗaukaka ƙara sun ƙare.Yanzu haka Silvio Berlusconi na fuskantar wasu jerin tuhuma, har guda biyu a kan almudahana da kuma yin lallata da wata budurwar.Tsohon firaministan na Italiya,na fuskantar matsin lamba na shari'a a daidai lokacin, da ake shirin gudanar da zagaye na biyu na zaɓuɓɓuka a ƙasar.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar.