1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Kotu ta yanke wa tsohon shugaban Colombia hukuncin dauri

August 1, 2025

Kotun ta kuma ci tarar tsohon shugaban kasar Alvaro Uribe dala dubu 578,000, baya ga daurin shekaru 12 a gidan yari.

https://p.dw.com/p/4yPku
Tsohon shugaban kasar Columbia Álvaro Uribe
Tsohon shugaban kasar Columbia Álvaro Uribe Hoto: Juan J. Eraso/ZUMA/IMAGO

Rahotanni daga birnin Bogota na cewa kotu ta yanke wa tsohon shugaban kasar Colombia Alvaro Uribe daurin shekaru 12 sakamkon samunsa da laifin cin hanci da rashawa da kuma gudanar da mulki ta hanyar da bata dace ba.

Karin bayani:Yarjejeniyar Kwalambiya ta bar baya da kura

Kotun Colombia karkashin jagorancin Sandra Liliana Heredia ta yanke wa Uribe daurin shekaru 12, kan zargin aikata manyan laifuka guda biyu, bayan an shafe sama da shekaru 13 ana gudanar da shari'a. Tsohon shugaban dai ya ki amincewa da aikata laifukan da ake tuhumarsa.

Karin bayani:Kwalambiya ta nemi 'yan kasar marasa takardu komawa gida daga Amurka

Babbar mai gabatar da karar ta ce nan gaba kadan kotun za ta duba yiwuwar yi masa afuwa ko kuma daurin talala a gidansa ko kuma tisa keyarsa zuwa kurkuku.