Kotu ta yanke wa Mohammed Badie hukuncin kisa | Labarai | DW | 11.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotu ta yanke wa Mohammed Badie hukuncin kisa

Wata kotu a Masar ta tabbatar da hukuncin kisa ga Mohammed Badie jagoran Ƙungiyar 'yan Uwa Musulmi.

Kotun ta yanke masa hukunci ne tare da wasu magoya bayan ƙungiyar su 11 waɗanda aka samu da lafin shirya kai hare-hare da kuma kitsa wa gwamnatin maƙarƙashiya don tayar da fitina.

Kotun dai ta bayyana wannan hukunci ne bayan da ta gabatar da shi ga jagorran addinin ƙasar kamar yadda dokar kasar ta tanada wato Mufti.Sannan kotun ta yanke hukuncin ɗaurin rai da rai ga wasu mutane su 23 a ciki har'da wani matashin ɗan ƙasar mai asilin Amirka wanda ake tsare da shi tun shekarun 2013.