Kotu ta tuhumi tsohon shugaban Chadi | Labarai | DW | 02.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotu ta tuhumi tsohon shugaban Chadi

Ana tuhumar Hissene Habre da aikata laifukan yaki da kisan ƙare dangi da kuma azabtarwa a kan jama'a a lokacin muklinsa Tsakanin shekarun 1982 zuwa 1990 a Chadi.

Da yake yinn tsokaci a kan tuhumar lauyan da ke kare tsohon shugaban Maitre Diouf ya ce :'' Habre na fuskantar wani al' amari ne, na sace shi da aka yi, kana aka yi garkuwa da shi, wanda kuma ya ce muke ɗora alhakin haka a kan wasu sojojin.''

Hissene Habre ɗan shekaru 71 a duniya na zaune a ƙasar ta Senegal tun a shekara ta 1990 lokacin da gwamnatinsa ta faɗi. Nan gaba ne dai kotun ta musammun da aka kafa za ta yi masa shari'a, a kan zargin da ake yi masa na aikAta kisa a kan mutane kusan dubu 40 waɗanda wasunsu suka mutu a gidajen kurkuku.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe