Kotu ta tuhumi Musharraf
August 20, 2013Jam'iyyar tsohon shugaban ƙasar Pakistan janar Pervez Musharraf ta yi watsi da hukuncin da wata kotu ta yanke na cewa Musharraf yana da hannu a kisan tsohuwar firimiyar ƙasar Benazir Bhutto. Kakakin jam'iyyar Musharraf, yace sun kaɗu da hukuncin kotun, ya ci-gaba da cewa ta yaya za'a ce shugaban ƙasa yana da hannu a kisan wani, don lamarin ya faru a mulkinsa kawai? don haka a faɗar kakakin jam'iyar janar Musharraf, wannan tuhumar shiri ne kawai. Kotu a ƙasar ta Pakistan dai, ta bayyana cewa janar Musharraf na da laifi, domin yaƙi baiwa Benazir Bhutto kariya ta jami'an tsaro yadda ya kamata, don haka za a yanke masa hukunci. Har yanzu dai akwai wasu laifukan da kotu ke tuhumar Muasharraf da aikatawa, waɗanda suma ba a kai ga cewa ko ya aikta ko a'a. Amma dai ko ba komai, masana suka ce wannan shine karo na farko da aka yankewa wani tsohon shugaban ƙasar Pakistan hukuncin aikta lafi, a ƙasar wanda tun samun yancin kai a shekara ta 1947, kusan duk sojoji ne ke mulkinta.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Mouhamad Awal Balarabe