Kotu ta tabbatar da hukunci ga Karim Wade | Labarai | DW | 20.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotu ta tabbatar da hukunci ga Karim Wade

Kotun kolin kasar Senegal ta jaddada hukuncin da aka yankewa dan tsohon shugaban kasar kuma tsofon minista Karim Wade na zama gidan kaso har na tsawon shekaru shida.

Tsohon Minista Karim Wade

Tsohon Minista Karim Wade

A watan Maris ne dai da ya gabata wata kotu ta yanke wa Karim Wade wannan hukunci tare da tarar kudi Euro milian 210, amma kuma lawyoyinsa suka daukaka kara a gaban kotun kolin kasar wadda ita kuma ta kara jaddada wannan hukunci ba tare da halartar Karim Wade din ko kuma lawyoyinsa ba. Kotun dai ta yi watsi da hujjojin da Karim Wade ya gabatar a gabanta na neman ta karya hukuncin da aka yi masa na ran 23 ga watan Maris, inda ya zargi alkallan da bangaranci, abun da kotun kolin kasar ta Senegal ta ce wannan zargi bashi da tushe balle makama. An dai zargi Karim Wade da laifin mallakar wasu tarin kudade da yawansu ya kai Euro milian 178 ba bisa hanyar gaskiya ba a lokacin da ya ke minista kuma mai bada shawara ga mahaifinsa Abdoulaye Wade a lokacin da ya ke shugaban kasa.